Canada: An kwashe mutanen wani birni saboda gobara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gobarar ta sa an kwashe mutanen wani birni gaba daya

Jami'ai a Canada sun ce tuni wata gagarumar gobara wadda ta yi sanadin da aka kwashe kafatanin al'ummar wani birni, ta jawo dumbin asara, kuma za ta iya ƙara muni kafin a shawo kanta.

An gaya wa mutanen da ke birnin Fort McMurray a Alberta su bar gidajensu saboda gobarar.

Masu kashe gobara sun ce kashi 80 cikin 100 na kaya da dukiya sun kone a wata unguwa, an kuma samu mummunar asara a wasu yankunan biyu.

An kawo wata tankar mai domin taimakawa masu motocin da suka maƙale a kan manyan titunan birnin.

Hukumomi na ta ƙoƙarin ganin an shawo kan ƙaƙƙarfar iska da take kaɗawa wadda ke kawo cikas wajen kashe wutar.

Karin bayani