Jami'an tsaro sun gana da Fulani makiyaya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana yawan zargin Fulani makiyaya da kai hare-hare

Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi wata ganawa da wakilan kungiyar Fulani makiyaya a kasar, wato Miyetti Allah.

A makon da ya gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa jami'an tsaron kasar umurnin ɗaukar matakin ladabtarwa, a kan makiyayan da aka samu da laifi a kashe-kashe da rikice-rikicen ƙabilanci kwanakin baya a wasu sassan kasar.

Wasu na zargin Fulani makiyaya da alhakin kashe ɗaruruwan mutane a Agatu na jihar Benue, zargin da makiyayan suka musanta.

Wakilinmu Abdullahi Kaura Abubakar ya tattauna da Brigadiya Janar Rabe Abubakar, kakakin shedikwatar tsaro ta Najeriyar domin jin ƙarin bayani kan abinda taron nasu ya tattauna a kai:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti