An soke takardar kuɗi ta Euro 500

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Babban bankin Turai ya soke takardar kudi ta Euro 500 bayan suka da wasu suke yi cewa, tana taimakawa wajen halasta kuɗin haram da kuma kaucewa biyan haraji.

Bankin wato ECB ya ce, zai daina samar da takardar kuɗin Euro 500 nan da shekaru biyu.

Za a maye gurbinta da ƙananan takardun kuɗi.

A Jamus inda yawancin jama'a sun fi son hada-hada da farin kuɗi sun ƙi amincewa da wannan mataki.

Sai dai masana na ganin da wuya wannan mataki ya daƙile halasta kuƙin haram.

Saboda a cewarsu, masu halasta kuɗin haram suna amfani da kamfanoni ne ba farin kuɗi ba.