Rasheed Yekini gwarzo ne — Fifa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rasheed Yekini lokacin da ya zurawa Bulgaria kwallo

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta ce dole ne ta yabawa tsohon dan wasan Najeriya, Marigayi Resheed Yekini, saboda shi ne mutumin da ya fara ciwa Najeriya kwallon farko a gasar kwallon kafa ta duniya, a 1994, da aka yi a Amurka.

A shafinta na intanet, Fifa ta ce kungiyar tana tuna kwallonsa da ya ci Bulgaria a wasan da suka tashi 3-0, a Amurka, a inda Yekini ya rike ragar yana girgizata cike da murna, bayan zura kwallon.

Rasheed ya taka leda a kungiyoyi daban-daban a Spaniya da Girka da Portugal da Switzerland.

Yekini ya ciwa Najeriya kwallaye 37, kuma shi ne ya lashe kyautar dan kwallon da ya fi kowanne na Afirka a 1993.

Tsohon shugaban hukumar ta Fifa, Sepp Blatter ya bayyana shi da " daya daga cikin 'yan wasan da suka fi kowa a gasar kwallon kafa ta duniya da aka yi a Amurka a 1994."

A ranar Juma'a, 4 ga Mayu 2012 ne dai Rasheed Yekini, mai shekara 48 ya rasu, bayan 'yar gajeriyar rashin lafiya.