'An daƙile harin IS a Kenya'

Hakkin mallakar hoto Kenya National Police Service
Image caption Har yanzu dai babu wata kafa mai zaman kanta da za ta tabbatar da wannan iƙirari da 'yan sandan Kenya suka yi.

'Yan sandan Kenya sun ce sun daƙile wani hari da wata ƙungiya mai alaka da ƙungiyar IS ta yi yunkurin kai wa a ƙasar.

An kama wani mutum da matarsa da kuma wata mace bisa zargi da hannu wajen yunƙurin kai harin.

An kuma sanya diyya ga duk wanda ya taimaka aka kama wasu mutum biyu.

'Yan sandan ba su bayyana sunan kungiyar ba, sai dai sun ce 'yan ƙungiyar suna cikin ƙasar da maƙwabtanta cikin su har da Somalia, Libya da Syria.

Har yanzu dai babu wata kafa mai zaman kanta da za ta tabbatar da wannan iƙirari da 'yan sandan na Kenya suka yi.