An kaddamar da manhajar adana hotuna

Hakkin mallakar hoto zakupki.gov.ru

An kaddamar da wata manhajar wayar salula inda za rika saka tsofaffin hotuna kuma a adana su.

Wasu 'yan Birtaniya biyu ne suka kirkiro manhajar da mutane zasu iya amfani da ita wajen saka tsofaffin hotunan iyalai.

Wadanda suka kirkiro manhajar suna aiki tare da hukumomin kare hakkin mallaka domin tabbatar da cewa, an san daga inda kowanne hoto ya fito.

Jama'a zasu iya sanya hotunan tarihi domin kowa ya iya gani, ko kuma su kebe dan wasu mutane kawai.