Ana jana'izar Papa Wemba

Ana gudanar da jana'izar Papa Wemba, daya daga cikin fitattun mawakan Afirka a birnin Kinshasa, na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Dandazon mutane ne ya taru a wajen babbar Cocin Notre Dame, inda ake yi masa addu'oi.

Idan anjima ne za a binne gawarsa a birnin na Kinshasa.

Wemba, wanda yake yi wa lakabi da Shugaban salon kida na rumba, ya mutu yana da shekara 66, bayan ya fadi daga kan dandamalin da yake waka a kasar Ivory Coast ranar 24 ga watan Afrilu.