An dambata a majalisar dokokin Afrika Ta Kudu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jam'iyyar adawa na son a tsige shugaba Jacob Zuma

An bai wa hammata iska a majalisar dokokin Afirka Ta Kudu yayin da aka fitar da wasu 'yan majalisar na ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun adawa daga zauran majalisar ta ƙarfi.

Suna ƙoƙarin kawo ruɗani ne gabanin wani jawabi da shugaba Jacob Zuma zai yi.

Wakilan jam'iyyar Economic Freedom Fighters, sun ce ba su ɗauke shi a matsayin shugaban ƙasa ba.

A watan jiya ne shugaba Zuma ya tsallake ƙuri'ar tsigewa lokacin da wata kotu ta ce ya saɓa kundin tsarin mulkin ƙasar.

Kuma a ranar Juma'a wata kotu ta ce a tuhume shi da laifin cin hanci.

Karin bayani