Ana ƙara tayar da jijiyar wuya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa

Image caption Wani harin kunar bakin wake da aka kai birnin Kudus a watan Afrilu ya hallaka mutane 20

A makon da ya gabata na koma birnin Ƙudus, mutane kaɗan ne suka tambaye ni abinda ya kawo ni. Na zaci ba ɓoyayyen abu bane.

Rikice-rikice da hare-haren da 'yan Isra'ila ke cewa Falasɗinawa na kai musu da kuma martani daga dakarun tsaro na Isra'ila, shi ne dalilana na zuwa don in shaida me ke faruwa.

Amma abokan aikina 'yan jarida suna nuna halin ko in kula.

Suna masu tambayar ko me ya sa sai a yanzu na je, bayan tun watan Oktobar bara ake rikicin?

Na zo birnin Ƙudus a kakar bara domin yin rahotanni a kan rikicin. Da irin sauye-sauyen da aka samu? A mafi yawan lokuta, idan abu ya dade yana faruwa, sai ya kasance ba labari ba ne a kafafen yaɗa labarai.

Amma kuma duk rikicin da zai zamo jiki ga mutane na haɗari sosai to ya kan ƙAra yin tasiri idan kafafen yaɗa labari suka mayar da shi babban kanun labaransu.

Rikicin dai na ƙara jawo wani mummunan yanayi tsakanin 'yan Isra'ila da Falasɗinawa. Hare-hare ya zama ruwan dare.

''Ƙiyayya tsakanin ɓangarori''
Image caption Diyar Rachel Dadon mai suna Eden ta kone sosai sakamakon harin bam

Eden Dadon 'yar Isra'ila mai shekara 15, tana kwance a wani asibiti a birnin Ƙudus sakamakon ƙuna mai tsanani a lokacin da wani bam ɗin Falasɗinawa ya fashe, a wata motar haya a ranar 18 ga watan Afrilu.

A lokacin da na haɗu da mahaifiyarta a asibitin, Eden ta shafe sama da wata guda bata cikin hayyacinta kuma an saka mata na'urar da ke taimaka mata wajen yin numfashi.

Rachel ta ce likitoci suna kokari su farfado da ita amma akwai wahala saboda 'yarta na fama da ciwo kuma ta kamu da cutar nimoniya.

Fashewar bam a cikin motar haya ƙirar bas na tunawa 'yan Isra'ila harin da yayi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan mutane a lokacin juyin-juya hali na biyu na Falasɗinawa bayan shekarun 2000.

Rachel, wacce dama a tsorace take kafin bam ya fashe a motar da suka shiga ita da 'yarta, bata da miji. Halin da 'yarta ta shiga ya tirsasata barin aikin kula da tsofaffi da take yi domin ta bai wa 'yarta kulawa.

A lokacin da take kallon bandejin da aka rufe ciwon 'yarta, Rachel ta yi korafin cewa babu wani daga ɓangaren gwamnati ko magajin gari da ya nema su. Tana yawan tunanin firgicewar da ta yi sakamakon harin.

'Ƙara fusata'
Image caption Dan Azar Abu Srour ne ya tayar da bam a motar bas inda har Eden ta kone sosai

Kamar ko da yaushe, ra'ayin Falasɗinawa ya banbanta sosai.

Na yi tafiya ta mil kaɗan daga birnin Ƙudus zuwa Beit Jala, wani ƙaramin gari da ke kusa da Bethlehem zuwa gidansu AbdulHamid Abu Srour, wani Bafalasɗine mai shekara 19 wanda ya tayar da bam ɗin da yayi sanadiyar fashewa a motar da ɗiyar Rachel Dadon ke ciki.

Ya ji rauni sosai bayan fashewar kuma ya rasa ransa bayan kwanaki kadan.

Dangin Abu Srour ba sa ƙawance da Isra'ila. Ana tsare da kawunnan Abdul su biyu a gidan yari na tsawon lokaci sakamakon kashe wani mai leƙen asiri na Isra'ila da suka yi. An harbe wani ɗan uwansa har lahira a wani rikici tsakaninsu da sojojin Isra'ila a watanni uku da suka wuce.

Dangin Abu Srour suna goyon bayan ƙungiyar 'yan ba-ruwanmu ta Falasɗinu wadda ake kira Democratic Front for the Liberation of Palestine.

Kungiyar ta kai munanan hare-hare a kan Isra'ila a shekarun1970, amma kuma daga baya sai ta shiga tattaunawar sulhu kuma a shekarar 1999 Amurka ta cireta daga cikin jerin sunayen ƙungiyar 'yan ta'adda. Duk kuwa da cewa 'yan Hamas sun ɗauki alhakin kai harin da Abdul ya kai.

'Wurin da rikicin ya fi tsananta'

A bangarori biyu na Isra'ila da su ka yiwa shinge a ciki da kewayen gaɓar yammacin kogin Jordan da yahudawa 'yan kama wuri zauna suka mamaye, suna da shakku a kan makomarsu. Akwai tsananin ƙiyayyar juna.

Image caption Wannan hoton da aka dauka a wani yanki da ke gabashin birnin Kudus na nuna sojin Isra'ila yana kallon kai kawon da ake a garin Beit Jala

Wani mai magana da yawun Firai ministan Isra'ila ya gaya min cewa, koyawa yaran Falasɗinu kiyayya ce ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke kawo harin 'yan ta'adda a kan fararen hular Isra'ila. Ya ce "Bai kamata hukumomin Falasɗinu su ɓata musu tunani da ƙiyayya ba.

Amma kuma tattaunawa da dama da Falasɗinawa a shekaru da dama da suka wuce sun gamsar da ni cewa babban abinda ya ke jawowa su ke nuna waɗansu irin ɗabi'u kan Israila shi ne, ba ainihin tsanar da Isra'ila take yi musu ce ke damunsu ba, amma mamayar yankunan Falasɗinawa wanda ya haɗa da gabashin birnin Ƙudus, da ya fara bayan nasarar da Isra'ila ta yi a gabas ta tsakiya a shekarar 1967, shi ne babban dalili.

Al'amuran ba sa sauyawa sosai a nan. Ƙasashen biyu sun shafe shekara da shekaru suna faɗa a kan fili guda ɗaya. Har yanzu dai shi ne babban maƙasudin rikicin.

An shafe shekaru 25 ana tattaunawar sulhu amma abin ya ci tura. Tashe-tashen hankula na baya-bayan nan na tsoratar da masu yawon bude ido da masu zuwa ibada, amma kuma 'yan Isra'ila da Falasɗinawa na cigaba da rayuwarsu kamar dai kullum.

'Yanayi mara tabbas'

Baya ga hare-haren kan tituna, babban abinda zai iya jawo rikicin duniya na cigaba da faruwa.

Ɗaya daga cikin abin da yake ƙara rura wutar rikicin shi ne, damar da yahudawa suke da ita ta shiga harabar masallacin Ƙudus. Tsaunin da masallacin ke kai kuma shi ne mafi tsarki a addinin yahudanci.

Tashin hankali na cigaba a kan iyakar Isra'ila da Gaza. An daina tattaunawar sulhu, kuma babu wanda yake yunƙurin sake farfaɗo da tattaunawar.

Sakamakon abin da hakan zai haifar shi ne sake dagula yanayin gaɓar Yammacin kogin Jordan tare da gabashin bienin Ƙudus. Akwai yiwuwar rikicin zai tsananta a kan yadda yanayin yake tun ƙarshen juyin-juya halin Falasɗinu na biyu, sama da shekaru 10 da suka wuce.

Tarihi ya nuna cewar duka bangarorin biyu suna ganin kamar babu wanda zai iya yin nasara a kan wani. Wata kila zasu iya yin yarjejeniyar sulhu wata rana.

Idan kuwa ba haka ba za su cigaba da fuskantar tsana da kuma yiwuwar ƙarin kashe-kashe.