Amurka: Kasich ya janye daga takara

Hakkin mallakar hoto AP

Mutum na ƙarshe da yake ƙalubalantar Donald Trump a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Republican John Kasich ya janye daga takarar.

John Kasich wanda shi ne gwamnan jihar Ohio ya bayyana janyewa daga neman takarar ne yayin wani taron manema labari mai sosa rai.

Wannan mataki dai ya share hanya kenan ga Donald Trump ya nemi shugabancin Amurka.

Bisa ga dukkan alamu kuma zai yi takara ne da ta gaba-gaba a jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton.

Yanzu dai Donald Trump ya ce, zai zaɓi mataimaki dake da ƙwarewar siyasa.