Za a yi taron ungozomomi na duniya

Hakkin mallakar hoto Getty

A Abuja babban birnin Najeriya yau ne ake buɗe wani babban taron ungozomomi na duniya.

Taron dai na zuwa ne a yayin da ake bikin Ranar Ungozomomi ta Duniya.

Ana sa ran taron zai tattauna hanyoyin samar da ungozomomin da za su taimaka wajen rage yawan haihuwar yara ba rai, da kuma mutuwar mata yayin haihuwa.

Hukumar al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, Nijeriya ita ce ta biyu a duniya wajen yawan mutuwar mata yayin haihuwa da yara ƴan ƙasa da shekara biyar.

An ƙiyasta cewa a cikin duk mata masu juna biyu 13 ɗaya na rasa ransu yayin haihuwa.

To sai dai kuma ungozomomi na fuskantar ƙalubale wajen gudanar da ayyukansu musamman a yankunan karkara.