'Fulani' sun sake kai hari a Zamfara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin jami'an tsaro kan lamarin amma ba mu same su ba.

Wasu mutane da ake zargi Fulani ne sun kai hari a ƙauyuka biyu da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum goma.

Mazauna ƙauyukan Madaɗa da Ruwan Tofa da ke ƙaramar hukumar Ɗan Sadau sun tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne ranar Laraba da asuba.

Wani Basarake a yankin ya shaida mana cewa maharan sun kashe mutum bakwai a Madaɗa, yayin da suka kashe mutum uku a Ruwan Tofa, kana suka jikkata mutum biyu.

Ya ƙara da cewa maharan sun je ƙauyukan ne a kan babura fiye da sittin.

Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin jami'an tsaro kan lamarin amma ba mu same su ba.

Yawan hare-haren da ake zargin Fulani da kai wa a yankuna da dama na ƙasar na ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya.

Hakan ne ma ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami'an tsaron ƙasar su dauki ƙwaƙƙkwaran matakai kan Fulanin da aka samu da hannu wajen kai hare-haren.