An samu 'yar nutsuwa a Aleppo

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni daga Aleppo da ke Syria na cewa an samu 'yar sa'ida tun shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Rasha da Amurka suka sanar a ranar Laraba.

Rundunar sojin Syria ta ce maslahar da aka samu za ta yi kwanaki biyu ce kawai.

Gwamnatin Syria dai ta bayar da rahoton cewa 'yan tawaye sun keta wasu dokokin tsagaita wutar, ta hanyar harba rokoki a wasu yankunan da ke karkashin ikon gwamnati.

Shugaban Siriyan Bashar al-Assad, ya ce sojojin kasar ba za su samu sukuni ba sai sun samu nasarar kama ikon Aleppo.

A wani bangaren kuma, tasoshin yaɗa labarai a Syria sun ce an kai harin ƙunar baƙin wake biyu a wani ƙauye da ke tsakiyar ƙasar, waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane shida.