Nigeria: An kashe masu satar shanu 18 a Zamfara

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Image caption Makaman da aka kwace daga wajen masu satar shanu

Sojojin Najeriya sun daƙile wani hari da masu satar shanu masu ɗauke da makamai suka sake kai wa garin Ɗansadau da ke jihar Zamfara.

Sojojin suna wani sintiri ne lokacin da wasu mutane suka sanar da su cewa sun ga maharan.

Daga nan sai tawagar sojojin ta yi wa maharan kwanton ɓauna wadanda suke kan babura ɗauke da makamai.

An gano cewa suna kan hanyarsu ta zuwa ƙauyukan Ruwan Tofa da Babban Doka ne a gundumar Ɗansadau ƙarkashin ƙaramar hukumar Maru, domin kai hari kan al'ummomin yankin.

Sojojin sun kashe 18 daga cikin maharan sun kuma ji wa wasu da dama raunuka.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Image caption Sojoji sun kona sansanin masu satar shanu a Dansadau

Sun kuma ƙwace bindigogi kirar AK47 11 da harsasai da bindigar toka da sauran muggan makamai.

Kazalika, dakarun sun lalata sansanin maharan da ke yankin Babban Doka.

Yanzu haka sojojin na karaɗe baki ɗayan yankin domin gano sauran maharan da suka ɓuya.

A sanarwar da rundunar sojin Najeriyar ta fitar, ta yi kira ga al'umma da su dinga taimakawa da bayanai kan masu satar shanu da 'yan bindiga da ma ko waɗanne irin masu aikata mugayen laifuka a yankunansu.