Bauchi: An zargi Yuguda da 'sace' biliyan 171

Gwamnnatin jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta zargi tsohon gwamnan jihar Malam Isa Yuguda, da yin sama da fadi da kudade kimanin naira biliyan 171.

Wani kwamiti da gwamnatimai ci ta kafa na bincike da kuma karbo kadarorin jihar daga tsoffin jami'an gwamnati, karkashin shugabancin Ritaya Air Commodore Tijjani Baba Gamawa ne, ya bankado wannan almundahanar.

Kwamitin ya mika rahotonsa ne ga gwamnan jihar Barista Muhammad Abdullahi Abubakar a ranar Laraba.

Kudaden dai sun shafi fannoni daban-daban da suka hada da tsaro, da harkar ilimi da kason kudaden kananan hukumomi da na shirin tallafa wa marayu da marasa galihu da dai sauransu.

Gwamnatin ta bukaci jami'an tsohuwar gwamnatin ciki har da tsohon gwamna, Isa Yuguda, da su mayar da kudaden ko kuma a gurfanar da su a gaban shari'a.

To sai dai jami'an tsohuwar gwamnatin sun musanta zargin almundahanar, inda suka ce gwamnatinsu ta yi aiki bil hakki ga al'ummar jihar.

Kakakin tsohuwar gwamnatin, Alhaji Salisu Ahmad Barau, ya kara da cewa zasu yi cikakken nazari kan zarge-zargen domin sanin martanin da za su mayar a hukumance.