Ana aikin ceto a Canada saboda wutar daji

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sama da masu aikin kwana-kwana dubu 11 ke kokarin kashe wutar.

Mahukunta a lardin Alberta na kasar Canada sun fara aikin ceton kimanin mutum dubu ashirin da biyar daga wani sunkuru a wani yanki mai arzikin mai, wadanda ke fuskantar barazanar wutar-daji.

Za a yi amfani da jirgin sama ne wajen kwashe kashi daya bisa ukun mutanen.

Mutanen yankin sun kasa tserewa ne saboda wutar-dajin ta yi musu kawanya, kuma tana ci gaba da ruruwa.

Sama da masu aikin kwana-kwana dubu 11 ke kokarin kashe wutar.

Firiministan lardin ya ce za a kwashe lokaci mai tsawo kafin wadanda gobarar ta kora su koma gida.