Sanatoci na so a yanke hukuncin kisa ga masu satar mutane

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate

Majalisar dattawan Nigeria ta nemi a yanke wa masu satar mutane hukuncin kisa sakamakon karuwar sace-sacen mutane da ake yi don karbar kudin fansa.

Wani dan majalisar dattawan, Abu Ibrahim, ya ce an sace mutane 225 a watan Oktoba da Nuwamba kuma sai da aka biya Naira miliyan 28 kafin a sako su.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnonin jihohi da su samar da dokar da za ta hukunta masu satar mutane da wasu laifukan da suka danganci irinsu.

Ta kuma bayar da shawarar a karfafawa Babban Sifeta Janar na 'yan sanda da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya gwiwar su kara kaimi wajen ayyukansu.