Rikici ya ci kujerar Firai Ministan Turkiyya

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Ahmet Davutoglu ya ce babu rashin jituwa tsakaninsa da Shugaba Erdogan.

Firai Ministan Turkiyya Ahmet Davutoglu ya ce zai sauka daga mukaminsa a lokacin da za a yi babban taron jam'iyyarsa ta AK nan gaba a wannan watan.

An yi amannar cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin Mr Davutoglu da Shugaba Recep Erdogan saboda kin amincewar da Davutoglu ga wasu shiryer-shiryen Erdogan na tsarin mulkin kasar.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, Mr Davutoglu ya sha alwashin yi wa Shugaba Erdogan biyayya, yana mai cewa babu wata rashin jituwa a tsakaninsa da kowa.

Za a sanar da mutumin da zai maye gurbinsa a lokacin taron jam'iyyar tasu ranar 22 ga watan nan na Mayu.