Bankin duniya ya bai wa Kaduna tallafin $21m

Hakkin mallakar hoto kaduna govt
Image caption Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa'i ya ce kudin tallafin kyauta ne.

A kokarinsa na inganta harkar ilimi, bankin duniya ya ba wa gwamnatin jahar kaduna Dala miliyan ashirin da daya domin gyara makarantu da kuma tallafa wa malamai da dalibai.

Bankin duniyar, wanda ya ce zai tallafa wa karin jihohin da ke arewa, ya ce zai sa-ido wajen ganin an yi amfani da wadannan kudade ta hanyar da ta dace.

Banki ya bayyana cewa bayar da wannan tallafi ya kunshi hadin kai da hadin gwiwa tsakanin masu bayar da agaji da kuma jihar Kaduna, domin bayar da ilimi tun daga tushe musamman domin yara mata.

Gwamnan jihar ta Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya ce bankin duniyar ya bayar da wannan tallafi ne domin a tabbatar da yara musamman mata sun je makaranta.

Malam Nasir el-Rufa'i ya cigaba da cewa wannan kudin da bankin ya ba wa jiharsa kyauta ne ba bashi ba, kuma kudin ya zo a dai-dai lokacin da ake bukatarsa.