Zimbabwe za ta fara buga 'Dalar Amurka'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zimbabwe ta yi watsi da takardar kudinta ne sakamakon tsananin hauhawar farashin kayayyaki.

Kasar Zimbabwe na shirin fara buga takardar kudin Dala irin ta Amurka domin rage karancin kudi da take fama da shi.

Shugaban babban bankin kasar John Mangudya ya ce takardar kudin, wacce ake kira bond a turance, za ta samu tallafin $200m daga bankin kasuwanci tsakanin kasashe.

Za a buga takardar kudin Dala biyu da biyar da Dala 10 da kuma Dala 20, wadanda darajarsu za ta kai daidai da kudin Amurka.

Kasar ta Zimbabwe ta kaddamar da fara amfani da takardar kudin Dalar Amurka ne bayan ta yi watsi da takardar kudinta a shekarar 2009 sakamakon tsananin hauhawar farashin kayayyaki.

Tun daga lokacin 'yan kasar ta Zimbabwe ke amfani da Dalar Amurka da kudaden wasu kasashen, cikin su har da kudin Rand na Afirka ta kudu da Yuan na China.