Bahaushe ya zama Kakaki a Bangui

Hakkin mallakar hoto

An zabi Abdou Karim Meckassoua, mai shekaru 63, a matsayin kakakin majalisar dokokin Afrika Ta Tsakiya.

An haifi Meckassoua a yankin Bangui ne, inda mafi yawan al'ummar musulman PK5 ke zaune.

Duk da mahaifinsa shahararren dan kasuwa ne, shi ma Abdou Karim din yana kasuwancin kazalika ya yi takarar zaben shugabancin kasar da aka gudanar a watan Disambar bara, ya kuma rike mukamin minista karkashin mulkin Shugaba Bozize har tsawon shekaru shida.

Ana masa kallon mai sassaucin ra'ayi kuma wanda zai iya hada kan al'umma, inda hakan zai taimakawa yunkurin kawo maslahar da shugaba Faustin-Archange Toudera ya dau alkawarin kawowa.