An tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Hakkin mallakar hoto
Image caption An tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce an tsawaita yarjejeniyar da aka cimma ta dakatar da bude-wuta a birnin Aleppo da kuma arewacin lardin Latakiya da ke Syria da karin kwana uku.

Rasha ta sanar da tsawaita yarjejeniyar ne da kwana uku, ana sauran mintoci wa'adin yarjejeniyar farko na kwana biyu ya cika, kuma Rashar ta yi haka ne gudun kada yanayin da ake ciki a Aleppo ya kara munana.

Kusan farar-hula 300 aka kashe a yakin da aka gwabza a cikin makwanni biyun da suka wuce, gabannin cimma yarjejeniyar dakatar da fadan.

An dai ba da rahoton cewa kura ta lafa a Aleppo, amma ana ci gaba da dauki-ba-dadi tsakanin sojojin gwamnatin Syria da mayakan An Nusra Front a kudancin kasar.

Yarjejeniyar dakatar da bude-wutar da aka cimma wani bangare ne na yunkurin da kasashen duniya ke yi da nufin fadada sulhun da aka yi tun a watan Fabrairu da ya gabata.