Zamu yi keke da keke wajen aiwatar da kasafi - Dogara

Hakkin mallakar hoto State House

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Hon.Yakubu Dogara ya ce majalisar dokokin ƙasar za ta bi diddigin yadda ɓangaren gwamnati zai aiwatar da kasafin kuɗin bana, domin tabbatar da an aiwatar da shi 100 bisa 100.

A bara dai ƙasa da kashi 40 cikin 100 na kasafin kuɗin ƙasar ne kacal aka aiwatar.

Mista Dogara ya faɗi haka ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan ya kammala zaman rattaba hannu kan kasafin kuɗin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi ranar Jumu'a.

Ya kuma ce majalisar ta fito da wani tsari na gayyatar ministoci lokaci-lokaci domin su yi bayani game da halin da suke ciki wajen aiwatar kasafin a ma'aikatunsu.

Ga ƙarin bayanin da ya yi wa manema labarai:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti