Kowa ya yi ta kansa — Erdogan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Erdogan yaki amincewa da tsarin EU

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya shaida wa ƙungiyar tarayyar Turai cewa ba zai sauya manufofinsa na yaƙi da ta'addanci ba, a madadin bai wa 'yan kasarsa izinin shiga Turai da tarayyar za ta basu.

Mista Erdogan ya ce, ''Su riƙe tsarinsu, mu ma mu riƙe namu.''

Tarayyar Turai ta ce Turkiyya na buƙatar sauƙaƙa manufofinta kan fassarar da ta yi wa ta'addanci domin 'yan kasarta su samu cikakkiyar damar tafiye-tafiye zuwa ƙasashen Turai.

Hakan dai na cikin wata babbar yarjejeniya tsakanin ƙasashen, da nufin rage rikicin ƙaurace-ƙauracen 'yan gudun hijira zuwa Turai.

Shugaban ƙasar ya faɗi haka ne kwana guda bayan Firai minista Ahmet Davutoglu,wanda ke goyon bayan yarjejeniyar ya yi murabus.

Karin bayani