An kai hari a kamfanin Chevron

Hakkin mallakar hoto Getty

Kamfanin mai na Chevron ya ce ya rufe wurin hakar mansa da ke yammacin yankin Niger Delta na Najeriya bayan wasu 'yan ta'adda sun kai hari a wurin.

Kamfanin dai ya ce yana tantance barnar da harin ya yi.

Chevron ya shaidawa jami'an tsaro aukuwar lamarin.

Kungiyar tsagerun yankin na Niger Delta ta sha alwashin durkusar da tantalin arzikin Najeriya idan har gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, tana mai cewa nan gaba za ta kai hare-hare a biranen Lagos da Abuja.

Babu cikakken bayani a kan bukatar kungiyar amma wasu kungiyoyin 'yan ta'addan sun yi korafi a baya cewa yankin na Niger Delta ba sa cin moriyar man da yake samarwa.