Shin wa zai zamo magajin garin Landan?

Wani bangare na sakamakon zaben magajin garin birnin London da aka gudanar ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar Labour Sadiq Khan, na dab da samun nasara akan abokin takarar sa na jam'iyyar Conservative Zac Goldsmith.

Matukar dai aka tabbatar da sakamakon nan da wasu sa'o'i, Mr Khan zai zama Musulmi na farko da ya taba samun wannan mukami.

Hakan zai karawa jam'iyyar Labour kwarjini tare da kawo karshen shekaru takwas da jam'iyyar Conservative ta yi tana rike da iko a birnin London.