Magajin garin Landan Sadiq Khan ya fara aiki

Musulmi na farko da ya kasance Magajin garin Landan karkashin babbar jam'iyar adawar Burtaniya ta Labour, Sadiq Khan ya sha rantsuwar fara aiki.

a wani biki a Southwark Cathedral dake birnin, Mr Khan dan wani direban bus dan cirani daga kasar Pakistan, ya ce yana zai wakilici ko wane bangare da al'ummar birnin.

Ya ce burinsa shine ya tabbatar da cewa daukacin mazauna birnin Landan sun samu damar da ya kamata ya samu.

Galabar da ya samu kan dan attajirnin nan takarar jam'iyar Conservative, Zac Goldsmith, na nuni da dawowar mulkin jam'iyar Labour a birnin na Landan, bayan shekaru takwas.

Sakamakon zaben dai zai kara wa shugaban jam'iyyar Labour, Jeremy Corbyn kwarin-gwiwa.

A baya dai jam'iyyar tasu ta fuskanci koma-baya a wasu zabukan da aka gudanar a kasar.

Sai dai jam'iyyar ta ba wa marada kunya dangane da hasashen da wasu ke yi cewa za ta yi mummunar faduwa a Ingila.