Amurka za ta sayar wa Nigeria jiragen yaƙi

Image caption Amurka ta sha alwashin taimaka wa Najeriya a yakin da take yi da Boko Haram.

Gwamnatin Amurka na shirin sayar wa Najeriya jiragen yaki domin kai hare-hare kan kungiyar Boko Haram da ta addabi kasar.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara ta musamman kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya tabbatar wa BBC cewa kasashen biyu suna tattaunawa domin sayar wa Najeriyar jiragen yakin samfurin Super Tucano.

Sai dai Malam Garba Shehu bai tabbatar da yawan jiragen da Amurka za ta sayar wa Najeriya ba.

A lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan dai, Amurka ta ki sayar wa Najeriya makamai da jiragen yaki saboda zargin da take yi wa gwamnatinsa da keta hakkin dan adam.

Tun lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan mulki, ya sabunta dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka, lamarin da ya sa Shugaba Barack Obama ya sha alwashin taimakwa kasar wajen murkushe 'yan Boko Haram.