Zika ta hana wasan kwallon baseball a Caribbea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dage wasa saboda harbuwa da cutar Zika

Wata babbar hukumar kwallon baseball ta dage wasu wasanninta daga birnin Puerto Rico na yankin Caribbean sakamakon fargabar da 'yan wasansu ke yi ta harbuwa da cutar Zika.

A karshen wannan watan ne ake sa ran kungiyar Pittsburgh Pirates za ta kara da Miami Marlins har sau biyu a San Juan, amma yanzu an mayar da wasan zuwa Miami.

A makon jiya aka samu mutum na farko da cutar Zika ta halaka a Puerto Rico.

An dai samu sama da mutum 600 da suka harbu da cutar a wannan tsibirin.