An sake bude masallaci a Bosnia

Hakkin mallakar hoto EPA

An sake bude masallacin yankin kabilun Serbia na Bosnia, da dakarun Serbia suka lalata lokacin yakin basasar tsohuwar Yugoslavia cikin karni na sha tara.

An dai gina masallacin na Ferhat Pasha ne tun a karni na sha shaidda a birnin Banja Luka, kuma ya dauki shekaru goma sha biyar kafin a kammala shi.

Injiniyoyin sun iya sake gano kusan biyu bisa ukun sauran duwatsun da aka gina masallacin da shi a baya.

Fiye da gwamman masallatan Banja Luka ne aka lalata a lokacin yakin, kana akasari musulmai sun tsere, ko kuma an tilasta musu barin yankin.

Shugabannin Sebia na Bosnia sun ce sake bude masallacin na nuni da yadda suke amincewa da sauran kabilu.