Gobarar daji a Kanada na iya habaka

Ana shirin kwashe karin dubban mutane zuwa tudun mun tsira sakamakon gobarar dajin da ke cigaba da ci a Alberta a Kanada wani lamari da ke zama kalubale mafi girma da yankin ya fuskanta.

Gobarar a yanzu ta bazu zuwa fiye da nisan kilomita dubu daya, sai dai jami'ai na baiyana fargabar cewa mai yiwuwa wutar ta kara habaka a yau fiye da halin da ake ciki a yanzu.

Wata 'yar siyasa a yankin kuma shugabar jam'iyyar adawa mai ra'ayin mazan jiya Rona Ambrose ta yabawa gagarumin aikin ceto da ke gudana yayin da 'yan jama'a daga kowane bangare na kasar ta Kanada ciki har da 'yan gudun hijirar Syria suke taimakawa wajen kwashe mutane 80 000 daga garin Fort McMurray mai arzikin mai.

A halin da ake ciki an dakatar da kimanin kashi daya cikin kashi hudu na aikin hakar man da Kasar ke hakowa a sakamakon gobarar.