Kwamde: Ana son kawo rudani da sunan Fulani

A Nijeriya yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan hare-hare da ake dangantawa da Fulani makiyaya, musamman bayan da wasu da ake zargin Fulani makiyayan ne suka kai hari da ake jin na ramuwar gayya ne a wasu kauyuka a jihar Enugu, inda aka samu hasarar rayuka, wani tsohon Jakadan Nijeriya a kasar Switzerland, ya ce ga alama wasu na neman sanya siyasa a cikin lamarin da nufin kawo rudani.

Ambasada Yahaya Kwande, wanda kuma ke daya daga cikin dattawa ‘yan siyasa a Nijeriya, ya ce Kodayake an dade ana samun rigima tsakanin manoma da makiyaya a Nijeriya, amma lamuran na baya-bayan nan, ga alama wasu ne daban ke neman kawo rudani, ta hanyar fakewa da sunan Fulani da kuma damar da suka samu sanadiyar yawaitar makamai a cikin kasar.

Ga dai Karin bayani da ya yi wa wakilinmu Is’haq Khalid

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti