Koriya ta arewa ta ce ba zata kai harin nukiliya kan kowa ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Koriya ta arewa ta ce ba zata kai harin nukiliya kan kowa ba sai anyi mata barazana ga 'yancinta

Shugaban Koriya ta arewa, Kim Jong-un ya ce kasarsa ba za ta kai harin nukiliya kan kowa ba sai an yi mata barazana ga 'yancinta.

Kafafen yada labaran kasar sun ambato Mr Kim na shaida wa babban taron jam'iyyar Workers Party mai mulkin kasar cewa akwai bukatar a kara tattaunawa da kasar Koriya ta kudu da nufin samun yarda da fahimtar juna.

Ya kara da cewa kasarsa za ta taimaka wajen hana yaduwar makaman nukiliya, duk kuwa da cewa kasarsa ta janye daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2003.

Shekara uku da janyewar Koriya ta arewar ne ta jarraba harba makamin nukiliyarta na farko, kuma ana yada jita-jitar cewa za ta jarraba makamin nukiliyarta na biyar a daidai lokacin da ake gudanar da babban taron jam'iyyar Workers Party.

Koriya ta arewar dai ta sha barazanar harba makamin nukiliyarta kan Amurka da Koriya ta kudu.