An cigaba da zanga zanga a Girka

Yan sandan kwantar da tarzoma Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan sandan kwantar da tarzoma na Girka

Dubun dubatar mutane suka halara a Athens babban birnin kasar Girka domin su ci gaba da zanga zangar kin amincewa da shirin yi wa tsarin fansho din kasar kwaskwarima.

Zanga zangar ta biyo bayan yajin aikin kwanaki biyu da aka yi kuma ta na zuwa ne gabanin kuriar da 'yan Majalisar Dokoki za su kada nan bada jimawa ba akan dokokin haraji da kuma fansho.

Zaftare yawan kudaden da kasar take biya a matsayin kudin fansho na cikin manyan bukatun kasashen duniya da ke samarwa kasar ta Girka da rancen kudi kafin su sake ba kasar karin talafi.

Ministocin kudi na kasashen Turai zasu yi taron gaggawa ranar Litinin domin su tattauna akan talafin da kuma bashin da ake bin Girka.