Majalisar dokokin Girka ta zartar da dokar Fansho da Haraji

Image caption Majalisar dokokin Girka ta zartar da dokar fansho da haraji

'Yan majalisar dokokin Girka sun zartar da wata doka mai cike da ce-ce-ku-ce, wadda ta yi tanadin garambawul da harkar Fansho da haraji, kuma zartar da dokar na daga cikin sharadin da aka gicciya wa kasar kafin ta samu kashi na gaba na tallafin farfado da tattalin arzikin ta.

Gabannin zartar da wannan kuduri dai an shafe kwanaki biyu ana tabka muhawara a majalisar, yayin da a bangare guda kuma aka yi zanga-zanga a wajen Majalisar.

Kungiyoyin kwadago sun ce kasar ba za ta iya jure wa wani tsarin tsuke bakin aljihun gwamnati ba, suna cewa mutum kalilan ne za su iya biyan haraji da kudin ajiyar fansho.

A yau ne ake sa ran Ministocin kudi na kasashe masu amfani da kudin Euro za su yi wani taro don tattaunawa a kan yadda Girkar za ta mayar da rancen.