Za a tallafi `yan gudun hijirar Nigeria

A Najeriya, ana sa ran aƙalla ƴan gudun hijira dubu ɗari biyar ne a arewa maso gabashin Najeriya za su amfana da wani shiri na hukumar samar da abinci ta duniya.

A ƙarƙashin shirin, wanda hukumar samar da abinci ta duniyar ta haɗa gwiwa da hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa, NEMA, da hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno, BOSEMA, da kuma hukumar kula da masu ƙaura ta duniya, IOM, za a riƙa ba da gudunmawar kuɗi duk wata ga iyalan da ke gudun-hijira, waɗanda ba a sansanoni suke ba.

Injiniya Satomi Ahmad shi ne shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno, ya ce kafin a fara bayar da tallafin, sai da aka kidaya kowanne magidanci aka kuma tantance su:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Injiniya Santomi ya kara da cewa za a bai wa kowanne magidanci N15,500 a duk wata, kuma za a shafe watanni shida ana ba su.

Yanzu haka dai an bayar da na wata guda, kuma ya ce za a cigaba da basu har sai an kai wa'adin da aka diba.