Dangote ya tallafa wa 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto b

Hamshaƙin attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote ya bayar da tallafin Naira biliyan biyu ga 'yan gudun hijirar da ke zaune a sansanoni a jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

Dangote, wanda shi ne ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirka, ya bayyana bayar da tallafin ne yayin ziyararsa a wasu sansanonin 'yan gudun hijirar da ke Maiduguri.

Attajirin ya ce cibiyar tallafin da ya kafa, wato Dangote Foundation za ta hada kai da gwamnan jihar Borno domin tantance irin tallafin da 'yan gudun hijirar ke buƙata.

Amma ya ce za a soma amfani da Naira biliyan biyu da ya bayar wajen samar da abinci da kuma ilimi ga 'yan gudun hijirar.

Alhaji Aliko Dangote ya kuma ce zai tallafa wajen ciyar da 'yan gudun hijirar a lokacin azumin bana.

Yayin ziyarar ta ranar Litinin Alhaji Aliko Dangote ya ganewa idanunsa halin da ake ciki a sansanonin Dalori da kuma Bakasi da ke cikin Maiduguri.

Rikicin Boko Haram dai ya raba dubban mutane da muhallisu a jihohin Borno, da Yobe, da Adamawa.