Alƙalai na yajin aiki a Niger

Hakkin mallakar hoto
Image caption Gwamnatin kasar ba ta ce komai ba tukunna kan yajin aikin

Ƙungiyar alƙalan jamhiryar Nijar, SAMAN, ta soma wani yajin aiki na kwanaki uku daga ranar Litinin, domin nuna rashin amincewarta da matakin ƙin mayar da wasu alƙalai bakin aikinsu da ministan shari'a

ya ɗauka.

Shugabannin ƙungiyar SAMAN sun ce yajin aikin wanda na ƙasa ne baki ɗaya ya samu karɓuwa.

Alƙalan dai an dakatar da su ne daga aikinsu bayan da suka yanke wani hukunci da bai yi wa gwamanan jihar Damagaran ɗadi ba a cikin watan Oktobar bara.

Sun bayar da belin wasu barayin dabbobi ne da aka kamo daga yankin Tanot a jihar Damagaram a watannin da suka gabata.

Mai shari'a Nuhu Abubakar, shi ne mataimakin kungiyar SAMAN, ga kuma abin da yake cewa kan matakin:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tuni jama'ar jamhuriyar ta Nijar suka soma nuna damuwarsu kan wannan lamari.

Ga ma yadda wasu 'yan kasar suka bayyana yadda yajin aikin ya shafesu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Wannan yajin aiki dai an fara shi ne a lokacin da ministan shari'ar kasar ya yi tafiya, amma wasu jami'an ma'aikatar sun tabbatar da cewa suna tattaunawa a kan lamarin.