An kwashe ma'akatan Shell daga Niger-Delta

Hakkin mallakar hoto Getty

Rahotanni daga Najeriya na cewa an kwashe ma'aikatan Shell a Bonga da ke yankin Niger-Delta a kudancin ƙasar, bayan wata barazanar ta'addanci da suka fuskanta.

A makon da ta gabata ne masu tayar da ƙayar baya suka kai hari kamfanin mai na Chevron da ke Nigra-Delta, inda ake cikin zaman ɗar-ɗar tun bayan da a watan Janairu gwamnati ta bayar da sammacin a kama wani tsohon shugaban 'yan tawayen yankin bisa zarginsa da cin hanci da rashawa.

Mazauna yankin na Niger-Delta dai sun jima sun buƙatar gwamnati ta ƙara musu kason kuɗin shiga na albarkatun man fetur.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu domin tsawaita wata yarjejeniyar afuwa da aka yi wa wasu 'yan tawayen Niger-Delta a shekarar 2009.

Amma kawo ƙarshen kwangila mai ƙwari da aka ba su ta kare bututan da shugaban ya yi ya sake tunzura 'yan tawayen.