Uganda: Kuɗin sayen littafi na iya zarta albashin wata guda

Samun littafin karantawa mai inganci a babban birnin Uganda ba aikin malalaci bane, kuma a zahiri kamar kasuwar bayan fage ce.

Mutane na neman masu zuwa ƙasashen waje domin su basu sallahun sayo musu littafin da ko dai yake da tsada ko kuma ba a samnsa a Kampala.

Wani littafin da ake ta son karantawa shi ne ''Nothing Left To Steal,'' wanda wani marubuci kuma dan jarida a Afrika Ta Kudu Mzilikazi wa Afrika, ya rubuta.

Amma kudinsa ya kai dala 42 a shagunan sayar da littafan ƙasar, kuɗin da zai iya sayen kayan abincin iyali na wata guda.

A kasuwannin intanet ana samun littafin da ake rububi da rahusa, amma kuma a kan samu matsala wajen aiko da shi Uganda.

Wakiliyar BBC Catherine Byaruhanga, ta ce ta taɓa sayen wani littafi ta shafin intanet, kan babban ɗan tawayen Guinea, Ahmed Sekou Toure, inda ta ce ta kashe dala 60, a yayin da ma'aikata a gidan sayar da abinci, da wuya su samu albashin da ya kai dala 60 a wata.

'Dillancin littattafai a kan babur'

A irin wannan yanayi ne Rosey Sembatya ta yanke shawarar ƙirƙiro da jerin littattafan tafi da gidanka, wanda ta sa wa suna Malaika Childrens Mobile Library.

Ta ce, "Ƴaruwata na da yara huɗu, kuma na yi ta samun matsalar saya musu littafi saboda tsadarsu."

Rosey ta ƙara da cewa, "Hakan ya sa nayi tunanin cewa akwai bukatar samun wata hanyar da zai basu damar samun littattafai cikin sauƙi."

Image caption ana biyan Rosey Sembatya dala 30 duk shekarar, kudin litattafai uku da yaran zasu karanta a mako daya.

Ɗakin litattafan na ɗaya daga cikin ɗakuna biyun da take haya a ciki, kuma ta jera ɗaruruwan litattafai bisa kanta, da faɗaɗan tebura.

Daga nan ne babura masu ƙafa uku ke ɗiban litattafan kuma su zagaye birnin suna bai wa yara damar karance-karance.

Misis Sembatya dai ta yi amfani da kuɗinta na ajiya ne domin gudanar da wannan ayyuka, kuma tana ƙoƙarin sassauta farashin saboda karatun yara.

A tsarin nata, idan aka biya dala 30 a shekarar, to yaro zai iya aron littattafai uku a sati.

Image caption Bookpoint kenan da ke Kampala sagon da sai ka iya zaton kana Landan ne ko New York, na kasashen Biritaniya da Amurka.

Amma kuma Uganda na da ma'aikatar wallafa littafai da dama, inda Fountain Publishers na ƙasar ke ɗaya daga cikin mafi girman ma'aikatar wallafa littafai a gabashin nahiyar Afrika baki ɗaya, kuma ta mayar da hankali ne kan rubuce-rubuce na boko.

A 'yan shekarun da suka gabata Christina Kakeeto ta bude shagon littattafai mai suna Bookpoint, a wata sabuwar kasuwa a Kampala, inda ta cika shagon da litattafan ƙasashen waje na Afrika.

Duk da cewar ta karancin aikin Injiya, Misis Kakeeto ta yi watsi da wannan aiki, ta mayar da hankali kan kasuwannin litattafai na ƙasashen waje, amma kuma kasuwa ce mai tsada ga yawancin al'ummar Uganda.

Image caption Abu ne wuya iyaye kamar Beverley Nambozo su iya saya wa yaransu littafai.
'Samun kwarin gwiwa'

Beverley Nambozo da mijinta sun zama darasi ga iyayen da ke son tabbatar da cewa yara sun girma da ɗabi'ar karatu.

Sun yi wa yaransu mata, Zion mai shekaru 7 da Raziela mai shekaru 4, rajista da kungiyarta Malaika Children's Library.

Beverley Nambozo, wacce ita ma marubuciya ce kuma ta san muhimmancin littafi, kafe da cewa karatu na da muhimmanci, domin shi ne hanyar da yara zas u samu rayuwa mai inganci.

Image caption Wasu 'yan Ugandan dai ba sa kyashin saya wa yaransu littafi, ko da kuwa su ba ma'abota karatun bane.

Karatu dai a Uganda sai in kana da kuɗi, amma idan har kana buƙatar aiki mai kyau, abu muhimmi ne ka zama kana da ilimi kuma ka iya karatun littattafai.