Bangladesh: An rataye jagoran babban jam'iyyar islama

Hakkin mallakar hoto BBC Bangla

An aiwatar da hukuncin kisa a kan jagoran jam'iyyar Musulunci mafi girma a Bangladesh.

An kashe Matiur Rahman Nizami ne, ta hanyar ratayewa, a babban gidan yari na Dhaka, babban birnin kasar.

Ya shafe shekaru goma sha biyar yana shugabancin jam'iyyar ta Jamaat-e-Islami, inda ya kasance na hudu cikin jerin shugabanin jam'iyyar ta Jamaat-e-Islami, da aka aiwatar da hukuncin kisa a kan su a 'yan shekarun da suka wuce.

An sami Mr Nizami, mai shekaru 73 da aikata laifuka kan bil adama a lokacin yakin da Bangaladesh ta yi na neman 'yan cin kai daga Pakistan a shekarar 1971.

A ranar Litinin kotun koli ta yi watsi da wani roko na karshe na sake duba hukuncin kisar da aka yanke masa