'Yar Biritaniya ta shiga Nollywood

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata kasuwa ta sayar da faifen fina-finai a Najeriya.

Wata baturiya 'yar Biritaniya mai harkar fina-finai ta samu wasan kwaikwayonta na farko a Najeriya, inda za ta fito a wani fim din barkwanci a dandalin fina-finan Nollywood da ke Legas.

Tafiya ce mai nisan gaske daga Winchester da ke kudancin Ingila inda Claire Edun ta fito,domin shiga dandalin na Nollywood.

Amma kam ba karamar tafiya ce Claire Edun, tsohuwar mai tarbar jama'a cikin jirgin sama, ke shirin yi ba.

Abunda ya kara sa ta zama ta musamman shi ne ta iya turancin Buroka, wanda wani harshe da ake magana da shi a Najeriya.

Fim din ta na farko a Najeriyar shi ne mai suna ATM, wanda zai fito Juma'a mai zuwa.

Yarinyar da aka fi sani da Princess Oyinbo (watau sarauniyar turawa) na shirin wasan kwaikwayon mai girma da alamu suka nuna zai yi matukar fice a Nollywood.