Nigeria ta shahara a cin hanci — Cameron

Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption Hukumar EFCC ita ce ke da alhakin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya

An naɗi Firai ministan Biritaniya David Cameron a hoton bidiyo yana shaida wa sarauniyar Ingila cewa shugabannin ƙasashen da suka yi ƙaurin suna a cin hanci da suka haɗa da Najeriya da Afghaistan na daga cikin waɗanda za su halarci taron yaƙi da rashawa a London.

Ba a dai tantance ko Mista Cameron ya san ana ɗAukarsa a bidiyo ba a lokacin da yake wannan magana a wani taro da aka yi a fadar Buckingham ta Ingila.

Da yake yi wa sarauniyar Ingila jawabi, Mista Cameron ya ce, ''Mun yi wani taron majalisa mai gamsarwa a safiyar Talata, inda muka tattauna kan taronmu na yaƙi da cin hanci da rashawa.''

Ya cigaba da ce wa sarauniyar, ''Shugabannin Najeriya za su zo, cikin baƙin namu har da shugabannin ƙasashen da suka yi ƙaurin suna a cin hanci.''

Sai ya ƙara da cewa, ''Nigeria da Afghanistan, ƙasashen da za a iya cewa su suka fi kowacce ƙasa matsalar cin hanci d rashawa.''

Ga dai bidiyon da aka dauki Mista Cameron yana wannan katobara:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Za a fara wannan taro kan cin hanci da rashawa ne a ranar Alhamis a birnin London.