Jam'iyya me ci a Cuba ta gayyaci APC kasarta

Hakkin mallakar hoto APC
Image caption Jakadan Cuba Carlos Trejo, tare da shugaban jam'iyyar APC ta kasa Cif John Odigie-Oyegun.

Jam'iyyar kwaminisanci ta Cuba ta gayyaci shugabannin jam'iyyar APC ta Najeriya zuwa kasarta.

Jakadan Cuba na Najeriya Carlos Trejo Sosa ne ya aike da sakon gayyatar a ranar Talata zuwa ga shugaban jam'iyyar APC na kasa Cif John Odigie-Oyegun.

A cikin wasikar, wacce ke dauke da sa hannun shugaban sashen harkokin cikin gida na jam'iyyar kwamanasanci na kasar ta Cuba, Jose Ramon Balaguer Cabrera, an bayyana cewa, "Muna wakiltar cibiyar kwamitin jam'iyyar kwamanasanci ta Cuba, kuma muna farin cikin mika hannun abotar al'ummar Cuba a gareku 'yan Najeriya tare da shugabancin dimokradiyyar da ke jagorantar ku."

Wasikar ta kara da cewa, "Muna da kwarin gwiwar cewa a karkashin shugabancin jam'iyyar APC, dangantakarmu da ta dade a tarihi za ta cigaba da yin karfi."

Jakadan dai ya ce gayyatar ta zo daidai da wani biki na kwanaki 30 da za a gudanar a Cuban kan murnar kawo karshen mallakar bayi a jamhuriyar Cuba.

Shugaban jam'iyyar APC ta Najeriyar kuma ya yi maraba da wannan gayyata, inda ya yaba dangantakar da ta jima tsakanin kasashen biyu.