IS ta fitar da sabbin haruffanta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar IS na son sanya yara a al'amuranta

Kungiyar IS ta fitar da wata manhajarta da ta kirkiro domin taimaka wa yara su koyi haruffan Larabci.

Sai dai kungiyar ta sauya alkiblar harkar ilimi ta yadda za ta dace da bakar aniyarta.

Alal misali idan yaro ya danna harafin ''B'' zai ji ta amsa da cewa ''B'' na nufin ''bundukiya'' -- wato bindiga kenan da Larabci.

Ko kuma ''D'' for ''dabaaba'' -- wato tanki da Larabci.

Ana ganin kirkirar wannan manhaja a matsayin wani misali na kokarin IS wajen sanya yara kanana cikin al'amuranta.