Buhari zai halarci taro kan cin hanci a London

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Shugaba Buhari ta tsare mutane da dama bisa zarginsu da hannu a karbar hanci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara a birnin London inda zai halarci wani taro kan yaki da cin hanci da kasashen duniya za su yi a Biritaniya.

Wata sanarwa da babban mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman kan watsa labarai, Malam Garba Shehu ya aikewa manema labarai, ya ce Shugaba Buhari zai tashi daga Najeriya zuwa Biritaniya ranar Talata, kuma za a fara taron ranar Alhamis.

A cewarsa, shugaban zai gabatar da mukala a kan yakin da gwamnatinsa ke yi da masu karbar hanci da rashawa a wata ganawa da za a yi gabanin taron.

Garba Shehu ya ce shugaban na Najeriya zai kuma yi jawabi ga manyan shugabannin duniya cikin su har da Firai Ministan Biritaniya David Cameron da shugaban babban bankin duniya Jim Yong Kim a kan muhimancin yaki da cin hanci da rashawa.

Kazalika, ana sa ran shugaban kasar zai yi kira ga mahalarta taron cewa ya kamata a jajirce wajen ganin an murkushe masu dabi'ar karbar hanci da rashawa.

Rahotani dai na cewa 'yan Najeriya da dama da ake zargi da hannu wajen sacen kudaden kasar, sun boye su a bankuna da dama na Biritaniya.