Rodrigo ya lashe zaben Philippine

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rodrigo ya yi ƙaurin suna wajen fatattakar masu aikata miyagun laifuka.

Mutumin da ke matukar yaƙi da masu aikata laifuka Rodrigo "Digong" Duterte ya lashe zaben shugaban kasar Philippine bayan 'yan takarar da ke hamayya da shi sun amince da shan kaye.

Babban abokin hamayyar Duterte, Mar Roxas , ya amince da shan kaye tun kafin a kammala fitar da sakamakon zaben ganin yadda Mr Duterte ya yi fintinkau.

Mr Duterte, mai shekara 71, ya ce ya karbi sakamakon zaben "Ina mai matukar ƙanƙan da kai".

Ya ce ya lashe zaben ne saboda alwashin da ya sha na tabbaatar da doka da oda.

Ya yi ƙaurin suna wajen fatattakar masu aikata miyagun laifuka a lokacin da yake magajin birnin Davao da ke kudancin kasar.