Buhari ya gaskata kalaman Cameron

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ba karya a zancen Cameron in ji Buhari

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce tabbas kalaman da Firai ministan Biritaniya ya yi kan cewa kasarsa ta shahara a cin hanci gaskiya ne.

Shugaba Buharin ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabi kan cin hanci da rashawa a sakateriyar ofishin kungiyar Common wealth, a birnin London ranar Laraba.

Ya shaida wa BBC cewa irin abubuwan da gwamnatinsa ta tarar lokacin da ta karbi mulki sun tabbatar da cewa kalaman Mista Cameron a kan hanya suke.

Da aka tambaye shi ko Najeriya ta 'shahara' a cin hanci da rashawa kamar yadda firai ministan Cameron ya fada, sai shugaba Buharin ya masa da cewa, ''kwarai kuwa.''

Ya kara da cewa zai zama kamar wani abin dariya ne ma ya musanta maganar.

''To idan ba haka bane ta ya ya gwamnatina ta kwato makudan kudade daga bankuna da kuma hannun wasu tsirarun mutane? Za mu mayar musu da kudinsu kenan idan muka ce maganar Mista Cameron ba gaskiya ba ce?"

Shugaba Buhari ya kara da cewa, ''Gaskiya ya fada. Ya fadi abin da ya sani ne ai."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A ranar Talata ne dai Mista Cameron ya shaida wa sarauniyar Ingila cewa Nigeria da Afghanistan na cikin manyan kasashen da cin hanci ya yi kamari a duniya, kalaman da suka jawo ce-ce-ku-ce.

Karin bayani