'Birtaniya ta dawo mana da kudadenmu kawai'

Hakkin mallakar hoto

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce shi dai ba ya bukatar a ba shi hakuri game da kalaman da Firayi Ministan Biritaniya David Cameron ya yi, inda aka dauke shi a bidiyo yana gaya wa sarauniyar Ingila cewa, Najeriya na gaba-gaba cikin kasashen da cin hanci ya yi wa katutu.

Da ya ke magana a wani taro game da cin hanci a birnin Landan, shugaba Buharin ya ce shi abun da ke gabansa shi ne mayar da hankali wajen kwato kadarorin kasarsa da aka boye a bankunan Biritaniya.

Mista Cameron dai ya yi katobarar ne a yayin da ya ke tattaunawa da sarauniya Elizabeth, a yayin da ya ke ma ta bayanin karbar bakuntan kasashen da zasu halarci wani taron koli kan cin hanci da rashawa da za a gudanar ranar Alhamis a birnin Londan.

Shugaba Buharin dai ya mayar da martani ne a lokacin da yake jawabi kan cin hancin da rashawar a sakateriyar ofishin kungiyar Common wealth ranar Laraba.

Da aka tambaye shi ko Najeriya ta 'shahara' a cin hanci da rashawa kamar yadda firai ministan Cameron ya fada, sai shugaba Buharin ya masa da cewa, ''kwarai kuwa.''

Ya kuma shaida wa BBC cewa irin abubuwan da gwamnatinsa ta tarar lokacin da ta karbi mulki sun tabbatar da cewa kalaman Mista Cameron a kan hanya suke.

''Gaskiya ya fada. Ya fadi abin da ya sani ne ai."

Mista Cameron dai shi ne ya shirya wannan taro da aka fara ranar Laraba kan cin hanci da rashawa a birnin London.