'Yan Nigeria 2 sun tsallake siraɗin gasar Caine

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tope Folarin, ya lashe gasar a shekara ta 2013

An bayyana sunayen marubutan da zasu fafata a gasar rubuta gajerun labarai ta nahiyar Afirka da ake kira Caine.

Kowacce shekara dai kwararru kan tace daruruwan labarai da suka shiga gasar har aka kai ga matakin bayyana wanda ya yi nasara.

Bana dai akwai 'yan Nigeria biyu da aka tantance labarun da suka rubuta.

Akwai kuma dan Somalia, ɗa ɗan Afirka ta kudu, da kuma dan Zimbabwe.

Dan asalin Nigeria, Tope Folarin shi ne ya lashe gasar a shekara ta 2013, kuma bana ma da shi za a fafata.

Gasar rubuta Caine dai an kafa ta ne da nufin jawo hankali ga marubuta 'yan Afirka da kuma bunkasa adabi a nahiyar Afirka.